Kamfanin Facebook wanda kuma ya mallaki WhatsApp da Instagram ya bayyana kudirinsa na dunkule shafukan 3 guri guda.
A wani rahoto da jaridar New York Times ta wallafa, ta bayyana cewa yin hakan zai baiwa masu amfani da shafukan damar sada zumunta da junansu, ta yadda ko da mutum yana da rajista da manhaja daya ne kadai a cikin ukun, zai iya zumunta da wadanda ke amfani da sauran.
Ma’ana, mai amfani da Instagram zai iya aika sako ga wanda ke amfani da Facebook.
Toh sai dai kuma da sauran aiki a gaba wajen tabbatar da faruwar wannan abu, kamar yadda kamfanin Facebook ya shaidawa BBC.
Ana tsammanin cewa za a kammala aikin ne nan da karshen wannan shekara ko farkon shekara mai zuwa.
No comments:
Post a Comment